Dan wan gaba na Paris Saint Germain Lionel Messi ya sake rubuta sunan sa da jan biro littafin tarihi na kofin duniya
Messi shine dan wasa daya fi haskawa a ‘yan wasan Argentina bayan nasara da Argentina ta samu 2:0 akan Mexico ranar Asaba. Dan wasan gaban Argentina (Messi)
shiya fara cin kwallo daga tazara bayan dawowa daga zagaye na biyu sannan daga bisani ya sake taimakawa dan wasan tsakiyan Benfica Enzo Fernandez bayan an kusa tashiwa.
A taimakon da Messi yayi akaci Mexico babban tarihi ne, ya zama dan wasa ‘daya tilo a tarihi da ya taimaka akaci kwallo a gasar cin Kofin Duniya na FIFA guda 5 daban-daban.
Gabadaya dan Wasan Argentinan ya taimaka anci kwallaye 6 a tarihin Kofin Duniyan sa. Yanzu yana bukatan ya sake taimakawa aci kwallaye uku kawai ya zarce Diego Maradona a wanda yafi taimakawa akaci kwallaye a tarihin Kofin Duniya. Messi zai fafata da Poland ranar Talata a wasan rukunin su na karshe.